Saudiyya ta hana jirage tashi a Yemen
November 6, 2017Talla
Wannan mataki ya sa hukumomin sufurin jiragen kasar Yemen suka sanar da soke dukkanin zirga-zirgan jirage a fadin kasar, matakin ya shafi tashoshin jiragen ruwa da na kasa da sauran hanyoyin sufuri na kowani bangare.
Wannan mataki baya rasa nasaba da sanarwar da dakarun kawancen Saudiyya suka fitar na rufe sararin samaniyar biranen Aden da Seyoun da ke yammacin kasar. Sojojin da Saudiyya ke jagoranta ne ke rike da iko a mafi yawancin yankunan da ke yammacin kasarb ta Yemen.
A tun watan Agustan shekara ta 2016, dakarun kawance karkashin jagorancin sojojin Saudiyya suka bada umarnin rufe babban fili jirgin saman kasar Yemen da ke Sanaa, yankin da ke hannun 'yan tawaye.
An sake bude filin jirgin saman Sanaa a YemenI S ta dau alhakin harin Yemen