Saudiyya ta kafa kawancen da zai yaki ta'addanci
December 15, 2015Kawancen da mai jiran gado na biyu a masarautar Saudiyya Yerima Mohammad Bin Salman ya sanar da kafashi, zai kunshi kasashen Musulmi zalla 34. Kuma zai dukufa kan yakar ta'addanci a duk kasashen Musulmi.
Bin Salman ya ce "wannan mataki mun daukeshi ne don nuna wa duniya irin himmar da kasashen Musulmi suke da ita don kawar da wannan cutar dajin da ke ci gaba da bazuwa musamman ma a kasashen Musulmi."
Talal Anbasi, dan majalisa a kasar Kuwait ya yaba wannan mataki, inda ya ce wannan sanarwa ta na da muhimmanci a siyasance da kuma a bangaren karfn soji.
Ya ce "A siyasance ilahirin kasashen na da fuska iri daya, yayin da a bangaren karfin soji kuwa, kawance na zama hannunka mai sanda ga kasashen duniya don su janye daga kasashen Musulmi, su barsu su magance matsalarsu da kansu."
Sai dai kuma rashin sanya kasashen Iran da Iraki da Syriya da Oman a kawancen, ya sanya wasu Larabawa suka fara tofin Allah tsine tun kafin a yi nisa.
"Wannan kawancen zai kara rura wutar rikicin bangaren akida a yankin. Kawance ya mayar da galibin kasashe mabiya tafarkin Shi'a saniyar ware. Idan ana so a yaki matsalar da ta shafi Musulmin duniya, sai an manta da banbancin akida da tafarki, kana a zama tsintsiya madaurinki daya."
Sai dai kuma Tayseer Atwan, jami'i a cibiyar dabarun yaki da ta'addanci a Lebanan ya rubuta a jaridar Assafir cewa, batun ba shi da alaka da akida, domin Oman na bin tafarkin Abadhiyya.