Saudiyya ta kai farmaki kan 'yan Houthis
May 16, 2019![Jemen Sanaa Luftangriffe der Saudis](https://static.dw.com/image/48758093_800.webp)
Talla
Wannan hari na zuwa ne kwanaki biyu bayan da 'yan tawayen kungiyar ta Houthis ta 'yan Shi'a masu samun goyon bayan Iran suka kai wasu hare-hare da jiragen marasa matuka na drone guda bakwai kan wasu kadarorin man fetir na kasar Saudiyya, harin da Saudiyyar ta dora alhakin kai shi ga kasar ta Iran.
A cikin wata sanarwa da ta fitar rundunar kawancen da Saudiyya ke jagoranta a yakin kasar ta Yemen ta bayyana cewa ta kai hare-hare ta sama a wasu cibiyoyin soji kasar ta Yemen da kuma a rumbunan ajiyar makamai na kungiyar 'yan tawayen Houthis.
Hukumomin kiwon lafiya a birnin na Sana'a sun ce mutane shida sun halaka, wasu gwammai sun jikkata a cikin wadannan hare-hare.