1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Saudiyya ta zargi Houthi da kai hari a Yemen

February 7, 2021

Jami'ai a kawancen Saudiyya da ke yaki a kasar Yemen sun sanar a wannan Lahadi cewa sun kama wani jirgi maras matuki shake da makami da aka yi niyyar halaka fararen hula da shi a yankin kudancin kasar.

Afghanistan | Air Force Drones
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/File/Lt. Col.. Leslie Pratt, US Air Force

Mai magana da yawun dakarun Saudiyya a Yemen, Turki al-Maliki, ya yi zargin cewa mayakan Houthi ne suka dano jirgin kuma dakarunsa ba su yi wata-wata ba wajen lalata shi.


Wannan ikirari da kawancen na Saudiyya ke yi na zuwa ne kwana guda bayan da Shugaban Amirka Joe Biden ya sanar da cewa zai janye sunan kungiyar Houthi daga cikin kungiyoyin ta'addanci na duniya. Ga shi kuma gwamnatin Amirkar ta ce daga yanzu za ta dakatar da janye tallafa wa kawancen Saudiyyar da ke yaki a kasar ta Yemen.