Saudiyya ta koma kai hare-hare a Yemen
May 18, 2015 Jiragen yaƙin Rundunar haɗin gwiwa ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta sun koma yin luguden wuta a kan mayaƙan Ƙungiyar Huthis ta 'Yan Shi'a waɗanda suka ƙwace milki a ƙasar Yemen.Wanann na wakana ne kwana ɗaya bayan da wa'adin tsagaita wuta na kwanaki biyar da rundunar hadin gwiwa ƙasashen larabawan ta ba da ya kawo ƙarshe.
Wasu majiyoyin Diplomasiyyar ƙasashen Turai sun ce hukumomin ƙasar ta Saudiyya sun sake komawa kai hare-haren ne a bisa zargin mayakan 'yan Huthis din da kin mutunta matakin tsagaita buda wutar inda suka yi amfani da wanann dama domin girka makamman atilare da na'urorin harba rokoki a kan iyakar ƙasar ta Yemen da ƙasar Saudiyyar.
Hukumomin sojan ƙasar ta Saudiyya sun ce sun lalata motocin yaƙi aƙalla biyar na mayaƙan Ƙungiyar 'yan Shi'an a cikin jerin hare-haren da suka ƙaddamar a wuraran da suka haɗa da fadar shugaban ƙasar ta Yemen da kuma a wani sansanin mayaƙan Ƙungiyar ta yan Huthis kai daga daran jiya zuwa washe garin yau litanin.sai dai ba su bada adadin mutanan da suka hallaka a cikin waƊannan hare-hare ba: