Zargin Yarima Salman da kisan Khashoggi
June 20, 2019Talla
Rahoton dai ya yi zargin cewa akwai hannun Yarima Mohammed bin Salman a kisan fitaccen dan jaridar da ke sukan masarautar Saudiyya. Mahukuntan Riyadh sun nunar da cewa rahoton na kunshe da kura-kurai da rashin son gaskiya. Wata jami'ar Majalisar Dinkin Duniyar Agnès Callamard ce dai ta gabatar da rahoton binciken, inda ta nunar karara cewa akwai bukatar a tuhumi yarima mai jiran gado na Saudiyyan Mohammed bin Salman dangane da kisan gillar da aka yi wa Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyan da ke birnin Santanbul na Turkiyya, tana mai cewa akwai alamu da ke nuna Yarima bin Salman na da hannu dumu-dumu a kisan.