Saudiyya ta rufe gadar da ta hada ta da Bahrain saboda Iran
April 7, 2026
Saudi Arebiya ta sanar da rufe gadar sarki Fahd, mai matukar muhimmanci da ta hada ta da kasar Bahrain, a wannan safiya ta Talata, sakamakon barazanar harin da Iran ta yi musu.
Sanarwar da hukumomin Saudi Arebiya suka wallafa a shafin X, ta umarci dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a kan gadar, mai nisan kilomita 25, domin kare rayukan jama'a da dukiyoyinsu daga fadawa tarkon hare-haren Iran.
Karin bayani: Isra'ila ta kashe babban jami'in leken asirin Iran
Wannan gada ita ce hanya tilo mai zuwa sansanin sojin ruwa na Amurka, mai kula da kasashen Gulf, wato Saudi Arebiya da Yemen da Oman da Hadaddiyar Daular Larabawa, sai Kuwait da Qatar da kuma Bahrain.
Karin bayani: Iran ta yi watsi da daftarin bukatu na tsagaita bude wuta
A wannan rana ta Talata wa'adin bude mashigin Hormuz da shugaba Donald Trump na Amurka ya bai wa Iran ke cika, ko kuma ya lalata dukkan cibiyoyin lantarkinta.
Karin bayani: Isra'ila ta kai wa babbar cibiyar makamashin Iran hari
Tuni rundunar sojin Isra'ila ta gargadi al'ummar Iran su kaucewa hawa jiragen kasa har zuwa karfe 9 na dare agogon kasar, a daidai lokacin da take shirin fara kai hare-hare kansu.
Wannan na cikin sakon da rundunar sojin Isra'ila ta wallafa a shafinta na X da harshen Farisanci, a wannan Talata.
Ita ko Iran ta umarci matasan kasar su taru a cibiyoyin lantarkin kasar, don ba su kariya daga hare-haren Amurka da Isra'ila.
Karin bayani:Senegal ta fara tsuke bakin aljihu saboda yakin Iran
A ranar Litinin, Iran ta sanar da kin amincewarta da sharuddan da aka gindaya, na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon kwanaki 45, tana mai cewar dakatar da yakin baki-daya take bukata kawai.