Saudiyya ta sallami 'yan cirani dubu 370
March 20, 2014Talla
Ma'aikatar cikin gida ta Saudiyyan ta ce 'yan ciranin sun fito ne daga kasashe daban-daban na duniya kuma an maida su zuwa kasashensu a tsakanin watanni biyar din da suka gabata, kazalika ma'aikatar a wannan Alhamis din ta ce ta na tsare da wasu karin mutane dubu 18 kuma nan gaba kadan za a maida su kasashensu.
Tuni dai masu kare hakkin bani adama na kasa da kasa suka fara kokawa dangane da wannan mataki da Saudiyyan ta dauka domin a cewarsu 'yan ciranin na shiga halin kunci a wuraren da ake tsaresu, ko da dai Saudin ta musanta hakan inda ta kara da cewar ta na sallamar bakin haure ne a wani mataki na samawa 'yan kasarta aikin yi.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal