Martanin Saudiyya kan matakin Amirka birnin Kudus
May 15, 2018Baya ma ga wannan matakin na Amirka a birnin Kudus, kasashe da dama dai na ci gaba da nuna damuwarsu kan kashe-kashen da Isra'ila ke yi wa fararan hula Falasdinawa. Daga nashi bangaren mai magana da yawun ofishin ministan harkokin wajen kasar China Lu Kang ya ce:
"China na nuna damuwa sosai ga karin mace-mace da ake samu daga bangaran Falasdinawa a tashe-tashen hankulan da ke guda a yankin Zirin Gaza, kuma China na mai adawa da amfani da karfi kan fararan hula masu zanga-zanga, sannan muna kira da a kai zuciya nesa."
Tuni dai daga nata bangare kasar Turkiyya ta bakin Firaministanta Binali Yildirim, ta yi kira ga kasashen musulmi da ke hulda da Isra'ila da su sake duba huldarsu, sannan Turkiyya ta yi kiran taron gaggawa na kungiyar kasashen Larabawa OIC a ranar Juma'a mai zuwa a kasar ta Turikiyya domin duba wannan lamari.