1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta yi barin wuta a sansanin Huthi

Binta Aliyu Zurmi MAB
December 26, 2021

Mayakan kawance da saudiyya ke jagoranta a kasar Yemen sun sanar da kai wani farmaki a sansanin mayakan Huthi da ke Sana'a babban birnin kasar a wannan Lahadi, inda suka kashe mutane uku.

Saudi-arabischer Luftangriff auf Sanaa
Hoto: Hani Al-Ansi/picture alliance/dpa

A cewar kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA, a wannan harin an yi nasarar lalata makamai da dama da ma mabuyar mayakan na Huthi. Wannan na zuwa ne bayan da a ranar Asabar, hukumomi a Saudiyya suka sanar da wasu harin rokoki da ake zargin mayakan Huthi da harbawa a masarautar Saudiyya wanda ya yi sanadin rayukar mutane uku da kuma jikkata wasu da dama. Harin da ke zama irinsa na farko ga masarautar a sama da shekarun uku.

Saudiyya dai ta jima tana zargin kasar Iran da daukar nauyin ayyukan mayakan na Huthi da ma samar musu da manyan makamai. Tun a shekarar 2014 ne Yemen ta fada cikin yaki tsakanin gwamnati da mayakan na Huthi da ke rike da ikon yankunan arewacin kasar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW