1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya: Mahajjata sun yi hawan Arafat

Abdul-raheem Hassan MNA
August 20, 2018

Sama da Musulmai miliyan biyu ne daga sassa daban-daban na duniya suka gudanar da tsayuwar Arafat a daidai lokacin da aikin hajjin bana ya kankama.

Saudi Arabien Mekka Pilger Berg Arafat
Hoto: picture alliance/dpa/Y. Arhab

Tsayuwa a kai ko gefen dutsen Arafat a ranar tara ga watan Zul-Hijja na zama kololuwa, kana abin da ya kasance wajabi a kan dukkan Mahajjata. A rana irin ta yau kimanin shekaru 1,400 da suka gabata, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, ya gabatar da hudubarsa ta bankwana a dutsen na Arafat.

Jami'an lafiya cikin shirin ko ta kwana a ArafatHoto: Getty Images/AFP/K. Sahib

Ana dai son dukkanin Mahajjata su gabatar da addu'o'i na musamman a wannan rana. Kuma a cewar wakilin DW Abdoulaye Mamane Amadou mahajjata sun himmatu da ibada duk da cewa ana yi a yanayi na zafi fiye da zafin da ake gani a kasashe kamar Nijar. Ya kara da cewa an tanadi jami'an kiwon afiya a ko'ina.

Ga batun tsaro kuwa an hana cinkoson mutane wuri guda, akwai kuma jiragen sama masu saukar ungulu, wadanda ke lura da zirga-zirgar jama'a domin tabbatar da tsaron lafiyar miliyoyin al'ummar da ke wannan ibada a kasa mai tsarki. Kwana guda gabannin ranar hawan Arafat, an yi ruwan sama da guguwa mai karfi da ta lalata tantunan Mahajjata amma hukumomi sun ce ba wanda ya jikkata.