1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Saudiyyya ta ki amincewa da kulla alaka da Isra'ila

Binta Aliyu Zurmi
February 7, 2024

Kasar Saudi Arabia ta shaida wa Amurka cewar ba za ta kulla wata huldar diflomasiyya da Isra'ila ba, har sai ta amince da kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta.

Saudiyya ta ce a samar da kasar da Falasdinawa za su kira ta su kamar yadda dokokin shekarar 1967 suka amince, da kuma sanya Gabashin Birnin Kudus, a matsayin babban birninta.

Kazalika sanarwar ta mahukuntan na Riyadh ta kara da cewar duk wannan ba zai yi wu ba har sai Isra'ila ta gaggauta dakatar da kai hare-harenta a Gaza da ma janye dakarunta daga Zirin gabaki daya.

Wannan sanarwar na zuwa ne bayan da mai magana da yawun fadar White House John Kirby ya bayyana wa manema labarai cewar tattaunawa sulhu tsakanin Saudiyya da Isra'ila na cigaba da gudana, kuma Amurka ta sami kyakyawan rahoto a kan yiwuwar amnincewar bangarorin biyu.

Dama dai Saudiyya ba ta cikin jerin kasashen Larabawa da su ka kulla yarjejeniyar kawance da Isra'ila a shekarar 2020.