Saura kiris Ukraine ta samu zaman lafiya - Trump
December 29, 2025
Shugaban Amurka Donald Trump da na Ukraine Volodymyr Zelenskyy, sun bayyana kyakkyawan fata cewa yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine na dab da samun amincewa daga kasashen biyu.
Shugabannin sun bayyan haka ne bayan tattaunawar da suka yi a jihar Florida, duk da cewa batun sallamar da yankunan Ukraine na ci gaba da zama babban kalubale.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawarsa da Zelenskyy a Mar-a-Lago, Trump ya ce Moscow da Kyiv sun fi samun fahimtar juna a yanzu fiye da kowane lokaci a baya, wajen cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
Zelensky na shirin sake ganawa da Trump
Trump ya kara da cewa an samu gagarumin ci gaba wajen kawo karshen yakin Ukraine kuma ya na sa ran kammala komai nan gaba.
A nasa bangaren, Zelenskyy ya ce an riga an amince da kashi 90% na yarjejeniyar zaman lafiya mai kunshe da abubuwa 20 da aka gabatar tun da farko.
Abin da Ukraine ta amince da shi
Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine ya ce zuwa yanzu kasarsa ta amince da jerin abubuwa da suka shafi yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninta da Rasha.
"Mun amince cewa tabbacin tsaro muhimmin ginshiki ne wajen cimma zaman lafiya mai dorewa, kuma kungiyoyinmu za su ci gaba da aiki kan dukkan fannoni." in ji Zelenskyy.
Steinmeier ya bukaci goyon baya ga Ukraine yayin Kirsimeti
Sai dai duk da haka, tattaunawar ba ta samar da wata gagarumar nasara a bayyane ba kan batun yankunan Ukraine, wanda ke da matukar sarkakiya.
Trump ya amince cewa har yanzu akwai batutuwa daya ko biyu masu “matukar wahala” da ba a warware ba, ciki har da matsayin yankin Donbas da ke gabashin Ukraine, wanda Rasha ta mamaye tare da hada shi da kasarta bayan kaddamar da cikakken farmaki a shekarar 2022.