Nijar: Sauya ministoci zai taimaka?
September 16, 2026
wasu daga cikin al'ummar Jamhuriyar ta Nijar dai na da ra'ayin cewa, ba ministoci hudu ne kawai ya kamata gwamnatin ta sauke ba. A ta bakin wasu da suka tattauna da DW, ya kamata idan za a yi kwaskwarima a tabbatar ba a nuna banbamci ba wajen saukewa da nadawa. Wasu na ganin akwai ministocin da suka yi ayyukan da ya kamata a yaba musu a majalisar, yayin da wsu kuma tun bayan juyin mulkin da sojojin kasar suka yi aka nada su kuma har yanzu ba a sauya su ba duk kuwa da cewa ba su taka rawar a zo a gani ba.
Kusan ko wacce shekar dai, ministocin na zuwa kafafen yada labarai su bayyana ayyukan da suka gudanar. Al'ummar kasar na yin alkalancin ayyukan ministocin, kuma al'ummar sun jima suna bukatar a yi gagarumar kwaskwarima a majalisar ministocin. Al'ummar dai na yin kira ga gwamnati da ta cika alkawuran da ta yi, duk ministan kuma da bai yi aiki kamar yadda aka bukata ba a sauya shi. Tun da fari, gwamnatin mulkin sojan ta kafa gwamnatin hadaka da fararen hula. An fara gwamnatin da ministoci 21, kafin daga bisani a kara yawansu zuwa 26.