Shugaban Najeriya ya sauya wasu ministoci
October 23, 2024Bayan share tsawo na lokaci ana ta hasashe, Shugaba Sauye-sauye ga majalisar ministocin Najeriya Najeriya ya yi wani garambawul bisa majalisar ministocin kasar. Ministoci guda biyar ne dai suka rasa aiki, a cikin sabon garambawul da ke zaman na farko ga gwamnatin Tinubu. A yayin kuma da shugaban ya sanar da nadin wasu guda bakwai a karkashin wani tsarin da Abuja ke fatan rage kisan kudi amma kuma ke kara yawan sunayen ministocin.
Karin Bayani: Cece-kuce kan yawon shugaba Tinubu na Najeriya
Ministocin da suka rasa aikin dai sun hada da Dr Jamila Bio Ibrahim da ke minista ta matasa, da kuma Abdullahi Mohammed Gwarzo da ke zaman karamin minista na gidaje. Ministan ilimin kasar Farfesa Tahir Mamman ma dai ya rasa aikinsa. An kuma sauke Lola Ade John da ke kafin yanzu ke zaman ministan shakatawa da bude idanu, sannan kuma da ministar mata ta kasar Barrista Uju-ken Ohaneye. Shugaba Tinubun dai kuma a fadar daya a cikin kakakinsa Abdul Aziz Abdul Aziz ya kuma nada wasu sabbabi na ministocin guda bakwai.
Ko bayan nadin sabbabi na ministan dai shugaban ya kuma sauya wurin aiki ga wasu, sannan kuma da sauyin fasali bisa wasu. Ministoci 10 ne dai suka fuskancin sauyin aikin da kuma suka hada da Dr Yusuf Tanko Sanunu da ya zamo karamin ministan jin kai, da kuma barrister Bello Mohammed Goronyo da ya koma karamin minista na aiyyuka. Imam sulaiman ce ta zamo sabuwar ministar mata a yayin kuma da Dr Doris Uzoka Anite ta zamo karamin ministar kudi ta Najeriya.
An dai hade ma'aikatar al‘adu ta kasar da ma‘aikatar bude ido da fasaha ta mawaka, a yayin kuma da aka rushe ma‘aikatar wassani ta kasar. Ita ma dai ma‘aikatar yankin Niger Delta ta koma ma‘aikatar raya shiyyoyi na kasar guda shida. Ana dai Kallon sabon sauyi da kokari na burge miliyoyi cikin kasar da suka share watani 16 suna zaman jiran tasirin Emilokan a rayuwa da makoma.