1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauyin salon zabar 'yan takarar gwamnonin APC

April 23, 2026

A yayin da ake dada nisa a cikin rikicin demokuraddiyar tarayyar Najeriya, gwamnonin da ke shirin barin gado na zaben masu gadonsu cikin mulkin jihohi.

Nigeria Maiduguri 2025 | Unsicherheit bedroht Nahrungsmittelproduktion
Hoto: Al Amin Suleiman Muhammad

 Akalla gwamnoni a jihohi 10 ne dai suke shirin adabo da kujerar gwamnan amma kuma ba tare da kau da kai a kokarin gadon nasu ba. Sabo na salon dai yana zaman ba sabunba a tarayyar Najeriya in da takara mai zafi ke zaman hanyar zabe na shugabanci a kasar.

Kama daga Ogun ya zuwa Nasarawa ko bayan jihar Kwara da ma ta Yobedai,  tuni gwamnoni na jihohin da ke shirin kammala wa‘adin mulkinsu suka fara nuna alamu na dauki dora na magadansu. An dai share tsawon wunin ranar Alhamis din nan ana kai kawo da nufin tabbatar da ko wane ne zai gaji gwamnan Yobe Maimala Buni.

Karin bayani: Rarrabuwar kawuna kan makomar gwamnan Bauchi 

Duk a cikin wata sabuwar dabara a siyasar tarayyar Najeriyar da ke sauyin launi da salo. Akalla gwamnoni 10 ne dai ke wa'adinsu na karshe kuma ke da babban burin dora masu gadon nasu ko ana ha maza ha kuma mata.

Hoto: Presidencia Villa Abuja

Ana dai kallon matakin gwamnonin da kokari na kaucewa rikici a cikin jam'iyyar APC da tai cikar kwari, kuma ke kallon buri iri iri cikin karfi na kudi da kila daurin gindi. Duk da cewar dai tuni wasu suka sa kafa suka shure tsarin daga dukkan alamu sabuwar dabar na neman burge wasu a cikin gidan jam'iyyar APC mai mulki.

Karin bayani: Zanga-zangar jam'iyyar ADC a birnin Abuja na Najeriya 

To sai dai kuma tun ba‘a kai ga ko'ina ba dai rikicin na neman mamaye matakin gwamnonin da daga dukkan alamu ba shi da goyon baya har cikin gidan na masu tsintsiyar. Sashe na 84 na dokar zaben tarayyar Najeriyar ta shekarar bana dai, ta tanadi zabe kai tsaye ko kuma ta hanyar sulhu kafin iya tabbatar da masu takarar gwamnoni a cikin jam'iyyu na kasar. Abun kuma da ya saba da dauki doran da ake gani cikin gidan gwamnonin yanzu haka.

Hoto: Presidencia Villa Abuja

Duk da cewar dai gwamnonin suna da karfin da ke neman wuce kima a cikin fagen siyasar Najeriyar a halin yanzu dai, daga dukkan alamu sabuwar dabarar tasu na da illar gaske ga kokarin kaiwa ya zuwa 'yanci na siyasar da 'yan kasar suke hankoron gani a zahiri. Dr Kabir Sufi dai na zaman kwarrare a siyasa ta kasar, kuma yace ne man nadi cikin gidan gwamnonin ya saba.

Karin bayani: Harkoki sun tsaya a Abuja saboda taron APC 

Koma ya take shirin kayawa a tsakanin masu kokari na dora magada da kuma tunanin bin doka dai, majiyoyi sun ce gwamnonin na neman kaucewa kokari na murde wuya na shugaban kasar da ke da burin gwajin farin jini a tsakani na masu tsintsiyar kasar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani