1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Najeriya na barar a yafe mata basussuka

September 5, 2022

A ci gaba dakokari na neman mafita kan bala'in sauyin yanayin da ke ta karuwa a Tarayyar Najeriya, gwamnatin kasar na neman lamuni na bashin da ake bin ta a ketare domin tunkarar matsalar.

Najeriya | Katsina | Ambaliyar Ruwa | Sauyin Yanayi
Ambaliyar ruwa da barazanar sauyin yanayi, ta sa Najeriya neman a yafe mata bashiHoto: DW/Y. Ibrahim

Kama daga sashen arewacin kasar zuwa na kudancinta dai, tasirin gurbata muhalli na kara fitowa fili da ma yin tasiri ga rayuwa da ci-gaban al'ummar Najeriyar. Gadoji na karyewa ko bayan rushewa ta gidaje da wanke gonaki, a wani abun da ke jawo asara ta dubban miliyoyin Nairori a cikin kasar da talakawanta ke kallon sarakuna, sarakunan kuma na fadin yanayi ba shi da kyau. To sai dai kuma gwwamnatin Najeriyar ta dauki sabuwar dabara da karkashinta Abujar ke neman a yafe mata bashin dubban miliyoyi na dalolin Amirka, domin samun damar tunkarar matsalar.

Karin Bayani: Bashi na son zamewwa Najeriya karfen kafa

Ya zuwa tsakiyar shekarar bana dai, dalar Amirka dubu 100 ke kan Tarayyar Najeriyar da sunan bashi. Kuma sama da kaso biyu cikin Uku na daukacin kudin shigar kasar, na tafiya ne a cikin sunan biyan kudin ruwa na bashin da ke ta karuwa. Mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya nemi bankin duniya da ragowar cibiyoyin kudi na duniya, su yafe bashin da fatan yin amfani da kudin wajen tunkurar matsalar sauyin yanayin. Osinbajo dai ya ce samar da lamunin da sunan alkinta muhalli na iya amfanar kasashe kamar Najeriyar da ke neman hanyar rage dimbin bashi da kuma manyan duniyar da ke neman rage bata muhalli.

Najeriya na daga cikin kasashen duniya da ke fama da matsalar dumamar yanayiHoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Umar Saleh Anka dai na zaman kwarrare a muhallin da ya kuma cikin mahallarta taron alkinta muhalli na Glasgow a shekarar da ta shude, kuma a cewarsa sabuwar dabarar ta dace da kokarin rage radadin matsalar. Ko ma wane tasiri sabuwar bukatar ke iya yi ga kokarin rage tasirin gurbata muhallin, a baya dai kasar ta kai ga samun lamunin da sunan inganta rayuwar al'umma ba tare da tasirin da 'yan kasar ke fatan su gani ba. A shekarar ta 2006 ne dai, manyan hukumomi na kudi na duniya suka yafewa kasar bashin da ya kai dalar Amurka miliyan dubu 24.

Karin Bayani: Najeriya ta talauce dole ne a ciwo bashi

To sai dai kuma har ya zuwa yanzu, ana kai kawo sakamakon komawar lamunin kafar wasoson 'yan boko ba tare da cimma burin sauya rayuwar 'yan kasar daga bashin ba. Dr Isa Abdullahi masanin tattalin arziki ne a Najeriyar, kuma ya ce da kamar wuya yafe bashin ya yi tasirin da 'yan kasar ke fata su gani. Sama da mutane dubu 500 ne dai, ambaliyar ruwan ta taba a shekarar bana a wani abun da ke kara fitowa fili da irin tasirin ssauyin yanayin.