Sauyin yanayi ya fi shafar kasashen Afirka
November 11, 2016Za mu fara sharhin jaridun na Jamus ne da matsalar sauyin yanayi wanda a labarin da ta buga jaridar Neues Deutschland ta ce faduwa ce ta zo daidai da zama da a yanzu haka ake gudanar da babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a wata kasa ta Afirka, domin wani rahoto a shekarar 2015 ya nuna cewa nahiyar ta fi ko wani yanki na duniya fama da matsalar sauyin yanyi.
Jaridar ta ce a gun babban taron da ke gudana a birnin Marakesh na kasar Maroko an gabatar da sakamakon wani bincike da ya nuna kasar Mozambik ta fi kowace kasa a duniya fuskantar masifar sauyin yanayi a bara, matsalar da ta janyo yawan mace-mace da kuma mummunan koma-bayan tattalin arziki. Fari na tsawon lokaci da ya haddasa karancin abinci da mutuwar dabbobi, amma ruwan sama mai yawa fiye da kima da ya biyo bayan farin shi kuma ya janyo ambaliya tare da lalata gonaki da gidaje. Haka lamarin yake a yankuna da dama na Afirka. A bisa wannan dalili ne kasashen Afirkar suka bukaci manyan kasashe masu ci gaban masana'antu da su kara yawan taimakon kudi da na fasahohi da suek ba su, domin kasashen Afirka su daidaita al'amuran tinkaran matsalar sauyin yanayin.
Lalalube cikin duhu kan matsalar 'yan gudun hijira
Sansanin karbar bakin haure a Afirka inji jaridar Süddeutsche Zeitung a sharhin da ta rubuta tana mai cewa:
Nahiyar Afirka ka iya zama wuri da ake sha'awar zuwa. Amma ba ga mutanen da ke kaura daga nahiyar zuwa Turai saboda dalilai na mulkin danniya da talauci da kuma yaki ba. Sai dai ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maiziére na son a rika komawa da 'yan gudun hijirar da aka ceto daga tekun Bahar Rum wuraren da suka fito. Wannan shawara ta sha suka. To amma bisa la'akari da dubban rayukan da ke salwanta a Bahar Rum za a iya yin fatan ka da su shiga jiragen ruwa marasa inganci, wato ke nan da zai fi dacewa kuma zai fi taimakawa idan aka samar da wani matakin tantance 'yan gudun hijirar da za a karba a Turan, tun a Afirka.
Ita ma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tsokaci ta yi kan matsalar gudun hijirar tana mai cewa a wani mataki na rage wahalhalun da masu yin kaura daga yankin Gabas ta Tsakiya da kuma Afirka ke fuskanta, ma'aikatar harkokin wajen Jamus da ta raya kasa za su samu karin kudi a badi karkashin wani shiri mai taken "Tallafi ga aikin jin kai a ketare" da yanzu haka aka ware wa kudi Euro miliyan dubu 1.2.
Bukatar fatun jakunan Afirka na karuwa a Sin
A karshe sai jaridar Berliner Zeitung wadda ta ce kasashen Afirka sun damu da yadda kasar Sin wato China ke kara bukatar fatun jakuna daga Afirka.
Jaridar ta ce shekaru masu yawa kasashe masu arziki ke tatsar arzikin karkashin kasa da Allah Ya huwace wa nahiyar Afirka. Yanzu an shiga wani sabon yayi inda kasar Sin da ta mamaye harkokin kasuwanci da dama a Afirka take kara nuna sha'awar kan jakunan Afirka, matakin da ya haddasa karanci da kuma tsadar jaki a kasashe da dama na Afirka, musamman a yankunan karkara, inda akasarin al'umma suka fi dogaro kan jaki wajen tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum.