1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauyin yanayi ya jawo karancin abinci a duniya

Fatima Ibrahim Mu'azzam
September 11, 2018

Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani rahoto cewar, ana samun karuwar mutane masu fama da yunwa sanadiyyar canjin yanayi da ake samu, wanda yake mummunar illa ga amfanin gona a yawancin kasashe masu tasowa.

Malawi World Food Programme
Hoto: picture-alliance/dpa/dpaweb/J. Hrusa

A rahoton da ta fitar a wannan Talata Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar an samu karuwar mutane milliyan 821 a shekara 2017 wadanda ke da bukata ta abinci sosai, idan aka kwatanta da mutane milliyan 804 da aka samu a shekarar 2016.Yayin da aka gano cewar kasar Afrika ta Kudu ita ce kasa da tafi kowacce yawan masu fama da yunwa a wani sako da David Beasley shugaban hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ya fitar.

Binciken rahoton ya gano cewar sauyin yanayin ya yi wa wasu albarkatun gona illa inda yake rage samar da alkama da shinkafa da masara. kuma ana tsammanin tsanantar yanayin a gaba idan ba a dauki mataki akai ba.

Haka zalika a shekaru uku da suka gabata duba da irin kunci da aka shiga na yunwa an kirayi hukumomi da su taimaka wa wadanda suke da bukatar taimako musamman mata da  kananan yara na al'ummar da canjin yanayin ya shafa.