Sauyin yanayi zai kara matsalar talauci a duniya
November 9, 2015Bankin Duniya ya yi gargadin cewa matsalar canjin yanayi da ake fuskanta za ta iya jefa mutane sama da miliyan 100 cikin ja'ibar talauci kan nan da shekaru 15 masu zuwa. Cikin wani sabon rahoto da ya wallafa, bankin ya bayyana cewa masu rayuwa hannu-baka hannu- kwarya ba su da matakan kare kansu daga cututtuka irinsu Malaria da fari da gurgusowar hamada da karancin abinci da sauransu. Saboda haka ne za su kasance a sahun farko na wadanda za su dandana kudarsu idan matsalar ta tsananta
Wannan rahoto ya zo ne makonni kalilan kafin taron koli da zai gudana a birnin Paris na kasar Faransa kan matakan kare duniya daka matsalar dumamar yanayi. Bankin Duniya ya ce idan ana so a raba talakawa da jin radadin matsalar sauyin yanayi, to ya kamata a inganta kiwon lafiyasu, tare da daukan matakan karesu daga matsalar ambaliyar ruwa da kuma lalacewar amfani gona.