1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cinikaya tsakanin Jamus da Angola

March 22, 2009

Cinikayya tsakanin Jamus da Angola

Angola ta ba Jamus Kwangilar ginin layin dogoHoto: picture-alliance / dpa


A ƙarshen watan Februaru na shekara ta 2009 ne, tawagogin ´yan kasuwa na ƙasasar Angola, tare da takwarorinsu na Jamus suka shirya wani mahimman taro a birnin Berlin na nan ƙasar Jamus.

A halin da ake ciki, Angola na ɗaya daga ƙasashen da tarmamuwarsu ke haskawa a nahiyar Afrika ,a game da cigaban tattalin arziki.

Bayan Nigeria, Angola ke matsayin ƙasa ta biyu a Afrika a game da albarkatun man Fetur.

Shekaru shida kacal da suka wuce ne a zo ƙarshen yaƙin basasa a ƙasar ta Angola, to amma tunni kasar ta himmantu wajen gudanar da aiyukan kyauttata rayuwar al´uma, da suka shafi gine-ginen hanyoyin asibitoci, makarantu da dai makantan su.

A dalili da wannan manyan aiyuka ne, ƙasashe masu zuba jari daga ƙetare mussamman China, Brazil, da Portugal da tayi wa Angola mulkin mallaka suka cya!! a ƙasar.

Kasar Jamus dake matsayin kasa mafi karfi ta fanin tatalin arziki a Nahiyar Turai ita ta duƙufa domin saka jari a Angola, ƙasashen biyu sun shirya taron na birnin Berlin wanda shine karo na biyu irinsa.

A ƙalla tawagogin kamfanoni da masana´antu 350 suka samu halartar taron daga ɓangarorin biyu.

A lokacin da ya gabatar da jawabi ministan tattalin arzikin Jamus Karl-Theodore zu Guttenberg ya bayyana mahimmanci saye da sayarwa tsakanin Jamus da Angola:

Ma´amilar cinikayya tsakanin Jamus da Angola, ta shiga wani yanayi mai inganci.

A watanni goma sha ɗaya na shekara da ta gabata, hajojin da muka sayo daga Angola,sun ƙaru da kashi 270 cikin ɗari, inda suka kai ga mizanin Euro miliyan 445.

A cikin wannan lokacin, hajojin da muka fitar zuwa Angola suma sun hau da kashi 15 cikin ɗari, zuwa ga mizanin Euro Miliyan 357.

A cikin ɗan ƙanƙanan lokaci, Angola ta kai ga matsayin ƙasa ta ukku a Afirka kudancin Sahara, ta fannin cinikaya tare da Jamus.

Tun shekaru 30 da suka gabata,shugaba Jose Eduwardo dos Santos ya hau kan karagar mulkin ƙasar Angola.Ya bayyana aniyarsa ta tada komadar tattalin arzikin ƙasar tun bayan ƙarshen yaƙin basasa da kuma fara tono man Fetur.

A yayin da ya gabatar da jawabi a taron, Dos santos ,yayi kira ga shugabanin kamfanoni da masana´antu Jamus, su shigo Angola a dama da su a wasu ƙarin fannoni na dabam da man Fetur.

Muna matuƙar shawar ƙulla sabin hulɗoɗi tare da kamfanoni da masana´antu Jamus, mussamman a ɓangaren gine- gine , noma da raya ƙasa,sannan muna shawar samun horo daga ƙurrarun masanan Jamus ta fannin bincike da kuma husa´ar zamani.

Babu shakka albarkatun man Fetur na sahun gaba daga hujjojin da suka sa cikin ƙibtawa da bisila, Angola ta fita daga sahun ƙasashe mafiya talauci a Afrika zuwa wanda suka samu cigaba, a shekara ta 2008, tattalin arzikin ƙasar ya bunƙasa da kashi 13 cikin ɗari.

A cewar Rainer Dzösch jami´i a hukumar ma´amilar cinikaya tsakanin Jamus da Angola, wannan kasa ta cencenci ayaba mata mussamman ta la´kari da yadda ta zama mattatara masu zuba jari daga kom iancikin duniya.

Idan aka duba yadda kamfanoni daga sassa dabam dabam na duniya ke fafatukar samun kwangila a wannan ƙasa, kai ka san da walakin.

ƙasashe kamar su China, Kanada, Turkiyya Isra´ila duk sun mamaye kasuwannin hada hadar Angola.

Shima Heiko Schwiederowski shugaban sashen dake kula da Afrika a cibiyar kasuwancin da masana´antu dake birnin Hamburg a nan ƙasar Jamus, kira yayi ga ´yan kasuwar Jamus kar su bari a bar su a baya,suyi amfani da damar dake akwai a ƙasar Angola, domin zuba jari:Angola na shirin gudanar da wasu mayan aiyuka da suka jiɓanci gina tashar jirgin ruwa, hanyoyin mota da na jiragen ƙasa.

Wannan dama ce ,ga kamfanonin Jamus da suka shahara ta fannin ƙarafa da husa´ar gine-gine, su shiga a damu da su.

To saidai mahimman albarkatun da Angola ke tamaƙa da sune lu´ulu´u da man petur wanda ke samar da kashi 85 cikin dari na kuɗaɗen shigar gwamnati, kuma a halin da ake ciki ,darajar man petur na cigaba da faɗuwa a kasuwannin duniya.

A dalili da wannan ,matsala gwamnati ta yanke shawara rage yawan man da take haƙowa daga ganga kussan miliyan biyu ko wace rana zuwa ganga ƙasa ga miliyan ɗaya.

Sannan ƙiddidigar da masana tattalin arzikin ƙasar suka gabatar, ta bayyana a baya, Angola na samun a ƙalla dalla miliyan dubu 65 ako wace shekara ta hanyar cinikin ɗanyan mai , amma a bana, dalili da halin da kasuwar man ta shiga Angola zata samu dalla miliyan 21 kaccal.

Budu da kari duniya baki daya ta tsinci kanta wani hali na taɓarɓarewar tattalin arziki, to saidai duk wannan, ba zai jawo illa ba ga hada-hadar kasuwanci a ƙasar Angola inji Andreas Wenkel na Afrika Verein wato hukumar dake kula da ma´mila tsakanin ´yan kasuwar Jamus da na Afrika.

Wenkel ya jaddada tasirin Angola a game da harakokin cinikayya da Jamus: Angola ƙasa ce mai mahimmanci a halin yanzu,ga kamfanoni da masana´antun Jamus mussamman saboda hajojin da take saye, a daya hannun Angola, ta kasance doli a dama da ita saboda dimbin albarakatunman petur da na Gaz da ta mallaka.

Saidai wani abunda ke ciwa masu saka hannayen jari tuwo ƙwarya a duk nahiyar Afrika, shine matsalar cin hanci da karɓar rashawa.

A rahoton da ta gabatar na shekara bara, Ƙungiyar Transparency International ta jera Angola a sahun ƙasashen da suka fi fama da wannan annoba, wadda taron birnin Berlin ba shi da maganin ta kuma sam bai ma ambato ta ba a cikin mahaurorin da aka shirya.

Ɓangarorin biyu sun bayyana gamsuwa ga sakamakon da taron ya cimma, idan aka auna yawan kamafanoni da masana´antu da suka samu halarta da kuma irin alƙawarna da suka ɗauka na lunka yawan hajojin da suke masanya a tsakanin su.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi/ J.Beck

Edita: Abdullahi Tanko Bala