1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ukraine: Turai ba za ta iya rayuwa babu gas daga Rasha ba

March 11, 2022

Scholz ya ce EU ba za ta iya gaggawar yanke wannan alaka a tsakaninta da Rasha ba kamar yadda Amirka da Kanada suka yi, domin su suna da makamashin gas da fetur a kasashensu.

Frankreich | EU Gipfel in Versailles | Olaf Scholz
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce Turai na kan aikin yadda za ta rage dogaro da man fetur da iskar gas na Rasha. Kalaman nasa na zuwa ne a tsakiyar dagulewar alaka tsakanin Turai da Rasha sakamakon kutsen da dakarun Rasha suka yi wa Ukraine. Sai dai Scholz ya ce katse sayen makamashi a hannun Rasha da gaggawa zai yi wa Turai wahala, abu ne da ke bukatar a yi shi a cikin lokaci.


Shugaban na gwamnatin Jamus ya yi wannan bayani ne a taron manema labarai bayan ganawarsa ta wannan Jumma'a da shugabannin Kungiyyar Tarayyar Turai a Faransa.