1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa kasuwanci a tsakanin Jamus da Najeriya

Binta Aliyu Zurmi MAB
October 30, 2023

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana aniyar fara sayo isakar gas daga Najeriya da nufin cike gibin makamashi da kasarsa ke fama shi tun bayan raba gari da Rasha sakamakon mamaye Ukraine da ta yi.

Nigeria | Bundeskanzler Olaf Scholz in Abuja
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a Abujan NajeriyaHoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana anniyarsa da samar da ingatacciyar hulda da Najeria ta fannin cinikayyar makamashin gas da sinadrin hydrogen.

A yayin babban taron da ya hada 'yan kasuwar Jamus da na Najeriya a birnin Lagos shugaban gwamnatin Jamus ya ce Najeriya na da kayataccen shiri kan makamashi, kuma kasar na da muhimmiyar rawar da za ta taka game da batun makamashin da ake sabontawa da iskar gas da sinadarin hydrogen wanda ya kara da cewa "Za mu cigaba da bukatarsu har nan da wasu shekaru a lokacin da kasuwarsa ta daidaita". Akwai kanfanoni manya da kanana na Jamus da ke ayyukansu a Najeriya, kana a sahun farko an amince da nagartar su ga misali Julius berger da sauransu a tsawon huldar da ke tsakanin Jamus da Najeriya ta fannin kasuwanci da ta kai shekaru sama da 60.

Karin Bayani:  Shirin inganta tattalin arziki a Najeriya

Shugaba Olasf kuwa da tawagarsa ta yan kasuwa ya tattauna batutuwan da suka shafi masanaantu kanana da tsaka tsaki musamman ga matasa 'yan kasuwar kasashen biyu, inda shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya jaddada bukatar da ke da akwai na karfafa tsarin kasuwancin nan marar shinge na bai daya da kasashen Afirka suka samar da ya soma aiki a farkon watan Janairun 2021.

Olaf Scholz  ya ce duk da yake tsarin na fuskantar tafiyar hawainiya a tsakanin kasashen Afirka 54 da suka amince da yarjejeniyar, shirin ka iya sawaka al'amurran kasuwanci da hada-hadar tattalin arziki a tsakaninsu ta hanyar janye haraji da wasu nau'in kudade da kasashen ke karba na fiton kayayaki, kana idan har tsarin ya dore zai kasance wani fagen da zai kasance na hada-hadar kasuwanci da cinikayya mafi girma a duniya domin yana kunshe da mutuane akalla miliyan dubu daya da 200.

Karin Bayani:  Scholz na Jamus na son fara sayen gas daga Najeriya

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da Bola Ahmed Tinubu a Abujan NajeriyaHoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

A yayin tattaunawarsu da shugaba Bola Ahmed Tinubu, shugaban gwmanatin Jamus Olaf Scholz ya bukaci hada karfi da karfe tsakanin kasashen biyu game da batun dawo da 'yan Najeriyar da ba su da takardun izinin zama kasar Jamus, ta hanyar inganta cibiyoyin da ke ba wa 'yan ci-ranin da aka mayar a gida kwarin gwiwar samun sana'o'i da ayyukan yi masu inganci, da ka iya kyautata musu rayuwa, matakin da Shugaba Tinubu ya ce Najeriya a shire take domin karbar 'yan gudun hijrar da ake kiyasta sun kai dubu 14 da ba su da takardun izinin zama Jamus. 

Wannan shi ne karo na 3 da shugaban gwamnatin Jamus ke kai ziyara a kasashen Afirka a kokarin fadada alakar kasarsa tun bayan darewa madafun iko kasa da shekaru biyun da suka gabata.

Bayan ganawa da mahukuntan na Najeriya shugaban gwamnatin Jamus Sholz zai je Lagos kafin ya karasa Ghana inda a can ma zai tattauna batuwan cinikayya a tsakanin kasashen.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani