1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Jamus ta amince EU ta daina sayen mai daga Rasha

May 1, 2022

Kungiyar EU ta jima tana kalllon dakatar da sayen makamashin a matsayin hanyar karya arzikin Rasha, domin hukunta kasar kan kutsen da take yi wa Ukraine. Amma kasashe irinsu Jamus kafin yanzu na dari-dari da matakin.

Berlin | Olaf Scholz
Hoto: Clemens Bilan/Getty Images

Kungiyar Tarayyar Turai, EU na duba yiwuwar sanya wa kasar Rasha takunkumin sayar da makamashi a gaba daya kasashe mambobinta. Sai dai wasu majiyoyi masu tushe sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Jamus, DPA, cewa shugaban gwamnati Olaf Scholz ya shirya amincewa da wannan matsaya.

Ita Jamus ta ce kawo yanzu ta rage yawan amfani da makamashin fetur da iskar gas Rasha daga kaso 35% a baya zuwa yanzu kaso 12% domin cimma wannan muradi, A taron da wakilan kasashen EU  za su yi a ranar Laraba mai zuwa ne dai ake sa ran Brussels za ta cimma matsaya a kan wannan takunkumi da ake ganin ka iya talautar da gwamnatin Shugaba Vladimir Putin na Rasha.