1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Scholz zai ziyarci garin da aka kashe mutane uku a Jamus

August 26, 2024

Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai ziyarci garin Solingen kwana uku bayan wani matashi ya daba wa mutane wuka.

Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz
Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Aurel Obreja/AP Photo/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus zai kai ziyara birnin Solingen a ranar Litinin kwanaki uku bayan da wani mahari ya daba wa mutane wuka.

A ranar Juma'a da yamma ne wani mutum ya kashe mutane uku tare da raunata karin wasu a tsakiyar birnin yayin bikin cika shekara 650 da kafuwarsa.

'Yan sanda sun bayyana cewa mutanen uku masu shekaru 56 da 67 da kuma 56 sun mutu ne sakamakon raunuka da suka ji sannan wasu takwas din kuma suna kwance a asibiti.

Shekaru 20 bayan kisan baki a garin Solingen

Ziyarar ta shugaba Scholz za ta fara ne da misalin karfe tara da rabi na safiyar Litinin inda zai fara da halartar addu'o'i ga mutane da aka halaka.

An tsare mutumin da ake zargi da kai harin mai shekara 26 kuma dan Siriya a yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.