1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Scholz zai ziyarci Turkiyya domin tattaunawa da Erdogan

October 11, 2024

Shugabannin biyu za su mayar da hankali ne kan rikicin Gabas ta Tsakiya da kuma tattalin arziki a tattaunawarsu.

Recep Tayyip Erdogan da Olaf Scholz
Recep Tayyip Erdogan da Olaf ScholzHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai ziyarci Turkiyya a mako mai kamawa domin tattaunawa da shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan.

Hukumomin Jamus sun ce shugabannin biyu za su tattauna ne kan rikicin Gabas ta Tsakiya da ke kara bazuwa da kuma ci-rani.

Ziyarar Scholz ta baya-bayan  nan a Turkiyya ita ce wacce ya yi a watan Maris na 2022, watanni kadan bayan ya kama aiki a matsayin shugaban gwamnati.

Karin bayani:Scholz ya ce Jamus na bukatar 'yan cirani

Shugabannin biyu za kuma su tattauna yakin Ukraine da harkar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu da suke zumunci tare da alakar kasuwanci.

Ko da yake yakin da Isra'ila ke yi da Hamas a Gaza ya dan fara shafar dangantakar kasashen inda wasu jami'an Jamus ke ganin akwai bukatar tattaunawa.

Karin bayani:Scholz zai ziyarci garin da aka kashe mutane uku a Jamus

Shugaban na Turkiyya dai ya sha caccakar Isra'ila kan yakin da ta ke yi a zirin na Gaza in da ya ce yaki ne na" kare dangi".