Schoof: Za mu tura 'yan Afirka da ke neman mafaka a Yuganda
October 18, 2024Firaministan Holland Dick Schoof ya ce gwamnatinsa mai ra'ayin mazan jiya na duba yiwuwar tura 'yan Afirka da aka ki amincewa da takardunsu na neman mafaka zuwa kasar Yuganda. Amma a bayanin da ya yi wa manema labarai a Brussels, Schoof ya yarda cewa ba mataki ne da zai yiwu ba saboda ana bukatar aiwatar da tsare-tsare masu yawa. Ba a fayyace ko irin wannan shirin zai dace da dokar kasar Holland ba, ko kuma Yuganda za ta amince da shirin tsugunar da masu neman mafakar ba.
Karin bayani: Jamus: Mayar da masu neman mafaka Senegal
Shirin na Holland ya biyo bayan tsarin da gwamnatocin Turai da dama ke neman aiwatarwa na tura masu neman mafaka a wajen kasashensu domin samun saukin mayar da su gida idan aka ki amincewa da bukatarsu. Dama dai rage kaurarowar baki na daga cikin manufofin da 'yan Holland da gwamnatinsu ke ba wa fifiko. Kusan mutane 50,000 da ke neman mafaka ne suka shiga kasar Netherlands ko Holland a shekara ta 2023.