1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SCHRÖDER YA YI WA TARON KASA DA KASA DA AKE YI A BIRNIN BONN JAWABI.

YAHAYA AHMEDJune 3, 2004

A yau ne shugaban gwamnatin tarayyar Jamus Gerhard Schröder, ya halarci taron kasa da kasa kan samad da makamashi maras gurbata yanayi da ake yi a birnin Bonn, inda ya yi wa wakilan kasashe mahalarta jawabi kan matakan da gwamnatinsa ke dauka wajen bunkasa wannan fasahar.

Shugaba Schröder, tare da ministocinsa na kare muhallli da na ba da taimakon raya kasashe, wato Jürgin Trittin da Heidemarie-Wieczorek-Zeul, yayin da ya iso a gun taron a Bonn.
Shugaba Schröder, tare da ministocinsa na kare muhallli da na ba da taimakon raya kasashe, wato Jürgin Trittin da Heidemarie-Wieczorek-Zeul, yayin da ya iso a gun taron a Bonn.Hoto: AP

A ci gaba da taron kasa da kasa da ake yi kan hanyoyin samad da makamashi maras gurbata yanayi a nan birnin Bonn, yau ne shugaban gwamnatin tarayya Gerhard Schröder, ya yi wa shugabannin gwamnatoci da na tawaga daban-daban da suka halarci taron, jawabi.

Da farko dai, shugaban ya bayyana wa mahalartan, muhimmancin birnin Bonn ne ga taron. Bonn, inji shugaba Schröder, ita ce ta cancanci shirya wannan taron, saboda a wannan birnin ne Hukumar Kare yanayi ta Majalisar dinkin Duniya ke da sakateriya dinta. Bugu da kari kuma, akwai kafofi da dama masu fafutukar kare muhalli da ke da cibiyoyinsu a tsohon babban birnin na tarayya. Don haka, shugaban na ganin cewa daidai ne, da birnin ya dauki nauyin karbar bakwancin wannan gagarumin taron.

Taron dai, inji Schröder ya kuma zo daidai a lokacin da ake bukatarsa. Irin matsalolin da ake huskanta wajen samad da makamashi, da kuma hauhawar farashin makamashin, kamar dai na man fetur da ake ta fama da shi yanzu, a duk duniya baki daya, sun sa wannan taron ya kara samun muhimmanci. Hauhawar farashin man fetur din dai abu ne da ke janyo cikas ga bunkasar tattalin arzikin duk kasashe, da kuma hana samun ci gaba a fafutukar da ake yi na yakan talauci da yunwa a duniya.

Shugaba Schröder ya kara da cewa, al’amuran da ke wakana yanzu a kasashen Iraqi da kuma Saudiyya, wato wani gangami ne ga kasashen duniya da su tashi tsaye, su ga cewa sun samo wasu hanyoyi daban-daban na samad da makamashi, don tabbatad da rayuuwar al’ummominsu. Sabili da haka ya ga ya kamata, a nuna misali a zahiri, da daukan sahihan matakai, don aiwatad da duk shirye-shiryen da aka tsara. In ko ba haka ba, to duk kasashen duniya ne wannan hauhawar farashin man fetur za ta shafa. Bisa cewar shugaban dai, a halin yanzu, hauhawar farashin man fetur ta baya-baya nan, ta janyo wa kasashe masu tasowa karin barnar kudi na kimanin dola biliyan 60. Tun ba aka kai ko’ina ba ma, kasashe mafi talauci a nahiyar Afirka, suna bad da fiye da rabin kudaden shigarsu wajen sayo man fetur. To bai kamata ba kuwa, kasashe mawadata su zuba ido suna kallon lamarin kamar babu abin da ya yi musu zafi. Duk mai son yakan talauci, in dai da gaske yake, to kamata ya yi ya zuba jari a fafutukar da ake yi na inganta hanyoyin samad da makamashi maras gurbata yanayi, wanda kuma a ko yaushe za a iya sabunta shi.

Gwamnatin tarayyar Jamus dai, inji Schröder, a shirye take ta nuna misali a zahiri, da daukan matakai wajen aiwatad da shirye-shiryen wannan fafutukar. Tuni dai tare da hadin gwiwa da wasu kafofin kudi na nan Jamus, gwamnati ta gabatad da wani tsari na bai wa kafofin da ke harkoki a wannan fannin tallafi.

Tun daga shekara mai zuwa, inji shugaba Schröder, gwamnatin Jamus za ta ware kudi na kimanin Euro miliyan dari 5, don bai wa kafofin kasashe masu tasowa tallafi wajen inganta wadannan hanyoyin na samad da makamshi a sawwake. Wannan kudin da aka ware dai, wato kari ne ga alkawarin da gwamnatin tarayyar Jamus ta dauka na ba da tallafin Euro biliyan diya ga shirye-shiryen, a taron da aka yi a shekara ta dubu 2 a birnin Johannesburg na Afirka Ta Kudu.

A cikin manyan bakin da suka saurari jawabin na shugabha Schröder, a zauren taron tsohuwar majalisar dokoki ta Bundestag da ke nan birnin Bonn, har da Firamiyan kasar Nijer, HAMA AMADOU, da shugaban Hukumar Kare Muhalli ta Majalisar dinkin Duniya Kalus Töpfer.