EU: Scotland na fatan sake koma wa
January 1, 2021Talla
Firaminstar yankin Nicola Sturgeon ta rubuta a shafinta na Twitter cewa: "Ba da jimawa ba Sotland za ta koma cikin EU, ku rubuta ku ajiye." Masu fafutuka na yin zanga-zanga cikin dare a Edinburgh da nufin neman ficewar yankin na Scotland daga Birtaniya domin samun 'yancin cin gashin kai. Yayin kada kuri'ar raba gardama dangane da ficewar Birtaniyan daga EU a 2016, da dama daga al'ummar yankin na Scotland sun zabi ci gaba da zama a EU din.