1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Senegal: A hukumance an tabbatar da zababben shugaban kasa

March 30, 2024

Bayan atyin murna da farin ciki da samun nasara a zaben Senegal da aka kammala a makon jiya, kotu a kasar ta tabbatar wa jagoran adawar kasar nasarar lashe zaben

Zababben shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye
Zababben shugaban Senegal, Bassirou Diomaye FayeHoto: Luc Gnago/REUTERS

Kotun tsarin mulki a Senegal, ta tabbatar da jagoran adawar kasar Bassirou Diomaye Faye a matsayin zababben shugaban kasa.

A cewar kotun Diomaye Faye ya lashe zaben da kashi 54% na kuri'un da aka kada a zaben karshen makon jiya.

Tsohon firaminitan kasar ta Senegal, Amadou Ba shi ne mutumin da ya zo na biyu a zaben a cewar kotun da kashi 36%.

Wannan matsayi na kotu dai ya kore rade-raden da wasu 'yan kasar ke yi game da yiwuwar zuwa zagaye na biyu tun da farko.

An dai sa ido sosai a kan zaben na Senegal ganin yadda kasar ta fama da darigizar siyasa kusan ta shekara guda.

A bara ne dai shiru din da Shugaba Macky Sall ya yi game ko zai tsaya takara a karo na uku ya haddasa bore a Senegal din.