1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani dalibi ta mutu a taho mu gama da jami'an tsaron Senegal

Binta Aliyu Zurmi
February 10, 2024

A ci gaba da arangama da jami'an tsaron kasar Senegal a jiya Juma'a rahotanni sun tabbatar da mutuwar wani dalibi a babban birnin Dakar.

Senegal Demonstration in den Straßen von Dakar
Hoto: Stefan Kleinowitz/AP Photo/picture alliance

Jami'an tsaron sun yi amfani da karfi da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa dandazon matasan da suka fito zanga-zanga.

Daruruwan masu boren ne aka ce bayan hatsaniyar ta barke suka yi ta jifar 'yan sanda da duwatsu.

Boren na jiya Juma'a ya yi sanadiyar rufe manyan hanyoyin birnin Dakar da na zirga-zirga jirgin kasa gami da kasuwanni.

Ko baya ga birin Dakar, an gudanar da zanga zanga a wasu biranen kasar, inda can ma jami'an tsaro suka yi amfani da borkonon tsohuwa wajen koran jama'a.

A farkon makon nan ne dai mahukunta a Senegal a karon farko suka sanar da dage zaben shugaban kasa, matakin da ya fusata al'umma.