1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Senegal da Benin na shirin ceto Kungiyar UEMOA

July 16, 2025

Kasahen Senegal da Jamhuriyar Benin sun yi alkawarin ceto kungiyar kasashen Yammacin Afirka masu amfani da kudin bai ta UEMOA daga matsalolin da suka dabaibaye tafiyarta.

CFA-Franc-Banknoten
Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images

Shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye da takwaransa na Jamhuriyar Benin Patrice Talon, sun ce za su dauki matakai a kwanaki masu zuwa domin samar da sabon numfashi ga Kungiyar kasashen yammacin Afirka masu amfani da kudin bai daya ta UEMOA, wadda ta fada cikin mawuyacin hali a baya-bayan nan.

Karin bayani: Rikici ya barke tsakanin kasashen AES da kungiyar UEMOA

Shugabani biyu sun yi wannan alkawari a ranar Talata bayan ganarwa da suka yi a birnin Cotonou fadar gwamantin Benin a yayin ziyarar aiki da Bassirou Diomaye Faye ya kai.

Kungiyar me membobi takwas ta jijjiga ne saboda rikicin siyasa da na manufa da ya dabaibaye yankin yammacin Afirka, bayan da kasashen Mali da Nijar da kuma Burkina Faso da ke karkashin mulkin sojoji suka raba gari da ECOWAS a madadin kafa kungiyar AES.

Karin bayani: Nijar na nazarin daina amfani da kudin CFA

Wadannan kasashe uku dai na da aniyar samar da takardun kudi na bai daya a tsakaninsu, sannan kuma sun shiga takun saka da kasashen Benin da Cote d'Ivoire da suke zargi da shuka musu makirci da hadin bakin Faransa.