1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal na shirin aiwatar da manufofinta

Abdourahamane Hassane
November 19, 2024

Jam'iyya mai mulki a kasar Senegal le Pastef, na kan gaba wajen samun gagarumin rinjaye a zaben majalisar dokokin kasar wanda zai bai wa Shugaba Diomaye Faye da firaministansa hanyoyin aiwatar da manufofinsu.

Hoto: Zohra Bensemra/REUTERS

 Tun farko gwamnatin Diomaye Faye ta fuskanci cikas wajen aiwatar da kasafin kudi  tun bayan zaben shugaban kasar saboda rashin rinjaye a majalisar. Daga cikin abin da gwamnatin za ta sake dubawa har da batun sake yarjejeniya cinikayya da kasashen ketare kan ma'adinai da sauransu. A hasahen da kafofin yada labarai dabam-dabam suka yi kan sakamakon wucin gadi na zaben, jam'iyyar ta Pastef na da kusan kashi uku cikin hudu na kujerun   majalisar 165.