1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Senegal ta lashe gasar AFCON

January 19, 2026

An karkare gasar AFCON karo na 37 cikin rudani da abin kunya a Maroko, inda Senegal ta dauki kofin a karo na biyu a tarihinta. Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka ta soke gasar CHAN ta 'yan wasa masu taka leka a gida.

Afrika-Cup 2025 | Finale | Senegal vs. Marokko | Brahim Diaz und Moussa Niakhate im Einsatz
Hoto: Sebastien Bozon/AFP/Getty Images

An wayi gari a Senegal cikin murnar lashe kofin AFCON a karo na biyu cikin tarihin kasar, bayan doke Maroko mai masaukin baki da ci daya mai ban haushi a gumurzu mintuna 120 da kasashen biyu suka fafata a filin wasa na Moulay Abdellah d ke birnin Rabat, wanda ya yi cikar kwari da 'yan kallo sama da 50,000.

Wasannin AFCON sun dauki hankali

Sai dai karawar ta bar baya da kura, domin ta kasance mai cike da rudani da kuma abin kunya saboda halin rashin da a da bige-bige da aka karkare fafatawar da su. Lamarin ya fara ne ana dab da tashi daga wasan bayan da Maroko ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida a minti na 96, abin da ya fusata 'yan wasa da magoya bayan Senegal saboda soke kwallon da Isma'ila Sar ya ci a minti na 93.

Hakan ya kai ga ficewar 'yan wasan Senegal daga filin wasa bisa umurnin mai horaswa Pape Thiaw. Wannan lamari ya bude babin muhawara kan alkalanci a nahiyar Afirka, sai dai dan wasa Brahim Diaz ya barar da wannan dama da ta hana mafarkin Moroko cika, bayan shafe kusan shekaru 50 tana hankoron lashe AFCON. Kasancewar Brahim Diaz gogaggen dan wasa mai kwakwa da naci da iya yanka, kuma da ya fito daga babbar kungiya.

Brahim Diaz ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida da Maroko ta samuHoto: Ulrik Pedersen/NurPhoto/picture alliance

Duk da yake an samu karafe-korafe a game da tsare-tsaren da Moroko ta yi na karbar bakuncin AFCON ta bana, amma hukumar CAF ta bayyana wannan karo na 37 na gasar a matsayin gagarumar nasara a tarihin kwallon kafa a nahiyar Afirka, imma a fannin baje kolin hazikan 'yan wasa ko kuma a fannin raya al'adun Afirka.

Haka zalika gasar ta zama wadda aka fi yin ruwan kwallaye a cikin tarihi, inda aka zuwa kallo 121 baya ga kuma kazamar riba da Hukumar Kwallon Kafar Afirka ta samu da ta rinbanya ta gasar da ta gabata har sau biyar. A yanzu kallo ya koma ga hukumar CAF domin ganin irin matakan ladabtarwa da za ta dauka kan Senegal, biyo bayan tarzomar da ta barke a kan idon duniya da kuma wasu kasashe da ma 'yan wasa da suka nuna rashin da a a lokacin gasar.

Shin ACF za ta dauki mataki?

Ana dai hasashen cewa hukumar CAF na iya cin Senegal tarar kudi da suka kai Euro 50,000 zuwa 100,000, tare da haramta wa mai horas da tawagarta Pape Thiaw halartar wasanni hudu zuwa shida, har ma da saka wa kasar takunkumin yin wasanni takwas a gida ba ta tare da 'yan kallo ba. A daura da AFCON Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka ta sanar da bijiro da sababbin tsare-tsare, domin kara bunkasa kwallo kafa a nahiyar.
Daga cikin tsare-tsare da shugaban CAF Patrice Motsepe ya sanar, har da soke gasar CHAN ta 'yan wasa masu bugawa a gida zalla. Gasar da aka samar shekaru 17 da suka gabata, ta kasance kafa da ke bai wai 'yan wasa masu taka leda a gida damar nuna bajintar da Allah ya ba su tare da bai wa na waje damar hango cancantarsu. A daidai lokacin da aka karkare AFCON kungiyoyi da dama a nan Jamus na dakon dawowar 'yan wasansu, ciki har da Bayern Munich da ke jiran dan wasanta zakaran nahiyar Afirka daga Senegal Nicolas Jackson.

Dan wasan Bayern Nicolas JacksonHoto: HMB Media/picture alliance

Lig na kasashen Turai

A daidai wannan lokaci Bayern Munich din na ci gaba da zama daram a kan teburin Bundesliga da maki 50, bayan ta bi RB Leipzig har gida ta yi mata dukan kawo wuka da ci biyar da daya. Ita kuwa Borussia Dortmund da ke rike da matsayi na biyu da maki 39 da kyar da jibin goshi ta kwaci kanta a hannun FC St Pauli, inda ta yi nasara da ci uku da biyu. Sai dai al'amura sun fara sukurkucewa Bayer Leverkusen bayan ta yi rashin nasara a gidan Hoffenheim da ci daya mai ban haushi, inda ta gangara zuwa matsayi na shida da maki 29, duk da cewa tana da kwantan wasa guda.

A Spaniya kuwa Barcelona ta yi daren kure a mako na 20 na La liga, inda ta sha kashi a hannun Real Sociedad ci biyu da daya. Wannan tuntube ya kawo raguwar ratar maki da Barca ta bai wa Real Madrid, daga maki hudu zuwa maki daya kacal.

Idan muka karkare da Premier Ingila Manchester City ta karbi kida a tattakin da ta yi zuwa gidan Manchester United a wasan mako na 22 da ci biyu da nema yayin da Nottingham Forest ta taka wa Arsenal da ke kan teburin gasar birki, inda suka yi canjaras babu ci. Ita ma Liverpool da ke a matsayi na hud da maki 36 ta gamu da turjiya daga Burnley, inda suka tashi wasa kunne doki daya da daya.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani