1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Senegal: Mata basu sami yawan mukamai ba

Abdoulaye Mamane Amadou
April 8, 2024

Rashin ba wa mata fifiko a rabon manyan mukamai cikin sabuwar gwamnati, ya fara tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin bangarorin siyasar kasar Senegal,

Präsidentschaftswahlen I Senegals regierende Koalition gesteht Niederlage ein
Hoto: John Wessels/AFP

Daukacin sababbin mambobin majalisar ministocin da aka yi wa lakabi da ta 'yan rajin kawo sauyi, bakin fuskoki ne, Sabuwar majlisar ta kunshi ministoci 25 da wasu manyan sakatarorin gwamnati, manyan mukaman da Shugaba Diomaye Faye ya fi la'akari da su a majalisar sun fi ta'allaka ne da na harkokin wajen da ma'aikatar iyali da matasa da da al'adu uwa uba da ma'aikatar kula da kamun kifi. 

Sabon firaministan na Senegal Ousmane Sonko, ya bayyana sabuwar majalisar ministocin a matsayin ta 'yan sauyi da kuma za ta yi kokarin biyan daukacin buktun 'yan kasar Seengal da suka kada wa kawancensu kuri'a.

"Gwamnati ce da ke shirin bi sau da kafa duk wasu bukatun al'umma na ganin an kawo sauyi da suka zaba tun a zagayen farko na zaben shugaban kasa wanda suka zabi shugaba Bassirou Diomaye Diakhar Faye a matsayin shugaban kasa."

Sabon firaministan Senegal Ousmane SonkoHoto: Sylvain Cherkaoui/AP/dpa

Sabon firaministan ya ce mambobin da shugaban kasar ya bukaci ya nada suna da gogewa ta fannonin ayyukan da aka dora musu alhaki, haka kuma za su dage don fitar da kitse daga wuta, sai dai wani hanzari ba gudu ba, shi ne mata hudu ne kadai ke da mukamai a sabuwar majlisar duk da gogewar da suke da ita ta kwarewa kan jagoranci da kuma fannin siyasa, lamarin da ya sa Nina Penda Faye wata kusa a kawancen kungiyoyin da ke fafutukar kare hakin mata ta ce ba a yi daidai ba.

"Irin wannan koken da ma korafin da muka yi wa gwamnatin da ta shude ne, haka za mu sake yi a yanzu, ganin cewa jawabin sabon shugaban ya karkata kan sauyi, kamata ya yi mu mata mu gani a kasa ta hanyar ba wa mata mukamai a cikin adalci da daidaito, mun lura kuma matan da aka ba wa mukamai a cikin sabuwar gwamnatin duk da yake basu wuce hudu ba, mukaman kuma da aka basu na da mutukar muihimmanci domin ba na yarwa bane."

Mata magoya bayan Ousmane Sonko a birnin Dakar na kasar SenegalHoto: Muhamadou Bittaye/AFP/Getty Images

Mukaman dai sun hada da na harkokin waje da na iyali da matasa da al'adu, haka da mukaman ma'aikatar kula da kamun kifi mai matukar kima da tasiri ga gwamnatin ta 'yan sauyi, dukacin mukaman na hannun mata ne, sai dai yawansu sun yi kadan kamar yadda  Fatou Bintou Sarr, wata kusa a jam'iyyar Pastef da ke mulkin Senegal ke cewa.

"Hudu daga cikin mukaman ministoci 25 gaskiya ne ya yi kadan amma kuma mu mata da kanmu ya dace mu tashi mu yi gwagwarmayar da ta dace don kwatar wa kanmu 'yancin da ya dace da mu,  fatanmu shi ne na ganin mata sun ciri tuta a fannin ilimi da kuma duk wata kwarewa da gogewa a fannin jagoranci, burinmu shi ne mu kara inganta kanmu da kanmu."

Doka dai a kasar ta Senegal ta yi tanadi daidaito a rabon mukamai a tsakanin jinsin maza da mata, sai dai kuma galibin dokar ana aiki da ita ne kawai a daidaikun hukumomi da ma'aikatun gwamnati sabanin amfani da dokar a kololuwar mukaman gwamnati da suka hada da ministoci.


To amma ga Djibril Gningue, wani mai fashin bakin siyasa a kasar ya ce duk da yake ba a yi raba daidai ba, sabon zubin na majalisar ministocin ya yi masa daidai.

Mata na bada gudunmawa a siyasar SenegalHoto: Muhamadou Bittaye/AFP/Getty Images

Idan aka yi la'akari da manufofin gwamnati da akidar da aka sa wa gaba a cikin wannan yanayi na sabuwar tafiya, to sai a  ce mambobin gwamnatin da aka nada Allah san barka, saboda wannan zubin ya gamsar da bukatunmu."

Duk da yake gwamnatin ta musanta yi wa mata kafar ungulu, domin ta na ci gaba da jajircewa da cewar mace ce ta farko a jerin manyan mukaman gwamnatin kasar baya ga firaminista.

Manyan ayyukan da gwamnatin kasar ta nuna cewa ta fi ba wa fifiko su ne matasa da mata da yaki da tsadar rayuwa baya ga batun kare hakkin bani Adama da tabbatar da doka da oda da hadin kan 'yan kasa.