1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal: Kokorin warware rikicin siyasa

August 5, 2023

'Yan majalisar dokokin Senegal sun fara zama a wannan Asabar don yin mahawara kan kundin zaben kasar yayin da ya rage kasa da watannin bakoye a gudanar da zaben shugaban kasa.

Hoto: Carmen Abd Ali/AFP/Getty Images

Sabon kundin zaben da ake mahawara a kansa, ya tanadi ba wa wasu manyan jagororin adawan kasar damar tsayawa takara, wadanda suka hadar da Khalifa Sall toshon magajin garin birnin Dakar da kuma Karim Wade da ga tsohon shugaban kasar kuma tsohon ministan sufiri da hulda tsakanin kasa da kasa.

A can baya dai dukannin wadannan 'yan adawa guda biyu ba su da damar yin takara a zaben shugaban kasa sakamakon zaman gidan kurkuku da suka yi kan badakalar kudade.

Ana dai kallon matakin na gwamnatin Senegal karkashin shugaba Macky Sall na sake dawo wa wadannan manyan 'yan adawa da rigar 'yancin tsayawa takara a matayin wani abu da ka iya taimakawa wajen warware rikin siyasar da ya barke a kasar yau da 'yan watanni.