1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Senegal: Sonko da Diomaye sun shaki iskar 'yanci

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim MAB
March 15, 2024

Afuwar da shugaban Senegal Macky Sall ya yi ne ta bayar da damar sakin 'yan adawan biyu, wadanda jam'iyyarsu ta tsayar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin dan takarar shugaban kasa, sakamakon haramta takarar Sonko.

Madugun 'yan adawa Ousmane Sonko na Senegal
Madugun 'yan adawa Ousmane Sonko na SenegalHoto: Seyllou/AFP

Jagoran adawar Senegal Ousmane Sonko ya shaki iskar 'yanci daga kurkuku, a wani bangare na afuwar da shugaban kasar ya yi wa 'yan siyasa, kwanaki kalilan gabanin zaben shugaban kasar, lamarin da ya jefa magoya bayansa cikin murna da sowa suna daga tututa da hotunansa a fadin kasar.

Karin bayani:Zanga-Zangar Senegal na ci gaba da janyo asarar rayuka

Lauyansa Bamba Cisse, ya bayyana cewa an saki Sonko da na hannun damansa Bassirou Diomaye Faye, bayan tsare su da gwamnatin Macky Sall ta yi a gidan yari tun cikin watan Yulin bara.

Karin bayani:Senegal: 'Yan adawa sun bakaci a saki dan takararsu

Jam'iyyarsu ta adawa ta tsayar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin 'dan takarar shugaban kasa, bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta haramta wa Ousmane Sonko shiga zaben, gabanin daure su.

A ranar 24 ga wannan wata na Maris za a gudanar da zaben kasar, bayan kwarbai na jeka-dawo da aka sha tun lokacin da shugaba Sall ya dage zaben watan Fabarairun da ya gabata.