Senegal ta ce za a yi wa tsohon shugaban ƙasar Cadi shari’a a birnin Dakar.
July 2, 2006Talla
Shugaba Abdoulaye Wade na ƙasar Senegal, ya ce ƙasarsa ta amince da shawarar da wasu ƙwararrun masana fannin shari’a na ƙungiyar Tarayyar Afirka suka bayar, ta yi wa tsohon shugaban Cadi Hissene Habre shari’a a ƙasar, inda yake zaune a halin yanzu.
Ƙwararrun masanan dai sun shawarci shugabanin ƙasashen ƙungiyar AUn ne, da su bari a yi wa Hissene Habre sahri’a a nahiyar Afirka, maimakon a miƙa shi ga ƙasar Belgium, wadda take zarginsa da wasu laifuffukan take hakkin bil’Adama.
Sakamakon wani binciken da gwamnatin Cadin ta sa aka yi dai na zargin gwamnatin Hissene Habre ne da yi wa kusan mutane dubu 40 kisan gilla da kuma azabatad da mutane kimanin dubu ɗari 2, a lokacin mulkinsa tsakanin shekara 1982 zuwa shekarar 1990.