1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal ta daukaka karar kwace mata kofi

Abdul-raheem Hassan
March 25, 2026

Kotun kolin wasannin kasar Senegal ta yi rajistar daukaka kara kan matakin CAF na kwace mata kambun AFCON don mayarwa Moroccco.

Afrika-Cup 2025 | Finale | Senegal vs. Marokko | Sadio Mané feiert mit Pokal
Tawagar 'yan wasan Senegal, lokacin da suka daga kofiHoto: Sebastien Bozon/AFP/Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta Senegal na kalubalantar hukuncin da hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ta yanke na kwace kambun da ta ci a gasar cin kofin nahiyar Afirka a karwarta da Morocco a wasan karshe mai cike da rudani wanda aka yi a watan Janairun 2026.

Gwamnatin Senegal ta yi alkawarin daukaka kara zuwa kotun sauraren kararrakin wasanni a kasar Switzerland, kuma ta yi kira da a gudanar da bincike na kasa da kasa kan zargin cin hanci da rashawa a CAF.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta CAS ta fitar ta ce, hukumar ta Senegal ta bukaci a ba ta karin lokaci domin shigar da karar saboda har yanzu CAF ba ta bayar da cikakkun bayanai a rubuce ba domin bayyana hukuncin da ta yanke. "A wannan matakin farko na shari'a da kuma la'akari da bukatar (Tarayyar Senegal) na dakatar da wa'adin, ba zai yiwu a yi tsammanin lokacin tsari ba da kuma nuna lokacin da za a saurara," in ji kotun.

Alkalan daukaka kara na CAF sun karbi kambun daga Senegal watanni biyu bayan kammala wasan karshe a Rabat a matsayin ladabtar da 'yan wasan da suka fita zanga-zanga a lokacin da aka dakatar da minti 15 bayan da Morocco ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Dokokin kwallon kafa sun bayyana hukuncin da alkalin wasa ya yanke kan filin wasa shine na karshe.
Alkalan CAF, duk da haka, sun ambaci dokar gasa cewa duk kungiyar da ta ki buga wasa "za a fitar da ita daga gasar da ake yi a yanzu." Hukuncin da aka yanke a makon jiya a karar da Morocco ta daukaka kan hukuncin ladabtarwa na CAF daga watan Janairu, ya kara rura wutar tunanin kasar da za ta karbi bakwancin gasar cin kofin duniya ta 2030, na kara yin tasiri a siyasar kwallon kafa ta kasa da kasa.