1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaAfirka

Sabbin matakan dakile coronavirus s Senegal

Suleiman Babayo AS
January 6, 2021

Gwamnatin kasar Senegal ta daukin sabban matakai kan dakile cutar coronavirus da suka hada da saka dokar hana fita da dare a manyan yankuna biyu na kasar.

Senegal Coronavirus Proteste in Dakar
Hoto: Reuters/C. van der Perre

Hukumomin kasar Senegal sun ayyana saka dokar hana fita da dare a yankuna biyu na kasar da suka hada da babban birnin kasar na Dakar, domin dakile yaduwar annobar cutar coronavirus.

Yayin jawabi ga al'mar kasar ta tashar talabijin Shugaba Macky Sall ya ce dokar za ta fara aiki daga wannan Laraba. Tun farko ministan kula da lafiya na kasar ta Senegal Abdoulaye Diouf Sarr ya ce kashi 90 cikin 100 na mutanen da suka kamu da cutar ta coronavirus suna yankunan biyun da aka saka wannan doka ta hana fita da dare. Tun aka bukaci mutane su yi amfani da kyallen rufe baki da hanci a wuraren taro da motocin safa-safa.