1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Senegal ta kama kwale-kwalen yan ci-rani mai shirin ketarawa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 20, 2024

Sojojin sun kama jirgin ruwan ne lokacin da suke sintiri a yankin da ake kamun kifi na Lompoul

Hoto: Leo Correa/AP Photo/picture alliance

Dakarun sojin Senegal sun sanar da kama wani kwale-kwale mai dauke da 'yan ci-rani sama da dari biyu, da ke yunkurin tsallakawa zuwa kasashen turai, kwanaki kalilan bayan mutuwar wasu guda 90 da suka yi kokarin shiga turai ta barauniyar hanya.

Karin bayani:An gano gawarwakin 'yan ci-rani guda biyu a cikin jirgin ruwan da ke dauke da mutane sama da 200 a Spain

Sojojin sun kama jirgin ruwan ne lokacin da suke sintiri a yankin da ake kamun kifi na Lompoul ranar Juma'a, dauke da mutane 202, ciki har da mace guda daya da karamin yaro daya, kamar yadda suka wallafa sanarwar a shafin X.

Karin bayani:Baerbock tana ziyarar kasashen Senegal da Cote d'Ivoire

A farkon watan nan na Yuli da muke ciki ne wani kwale-kwale dauke da mutane 170 ya kife a cikin gabar ruwan Mauritania, bayan tasowa daga Senegal, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 90 daga cikinsu.

Wata kungiyar agaji ta kasar Spain mai suna Caminando Fronteras, ta ce mutane sama da dubu biyar ne suka rasa rayukansu a watanni biyar na farkon wannan shekara, sakamakon kokarin shiga turai ba bisa ka'ida ba.