1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal ta karbi kason farko na rigakafin Corona

March 3, 2021

Senegal ta bi sahun wasu kasashen Afirka da suka karbi alluran rigakafin corona wadanda Hukumar Lafiya ta Duniya ke bai wa kasashe matalauta cikin shirinta na COVAX.

Impfkampagne in Südafrika
Hoto: Siphiwe Sibeko/AP Photo/picture alliance

Kasar dai ta karbi kimanin allurai dubu dari uku da 24 daga cikin miliyan daya da dubu 300 da aka tsara ba ta, kari a kan allurai dubu 200 da kasar ta sayo daga China don kaddamar da kashin farko na rigakafin.

Kimanin mutane dubu 40 ne dai ciki har da Shugaba Macky Sall aka yi wa allurar rigakafin a Senegal tun bayan kaddamar da ita a makon da ya gabata. 

Kasar mai yawan al'umma miliyan 16, na sa ran yi wa akalla mutane miliyan uku da rabi rigakafin na corona nan da karshen wannan shekarar wanda za su hada da ma'aikatan kiwon lafiya da masu hadarin saurin kamuwa da cutar da ma mutanen suka manyanta.

Kazalika a wannan Laraba, ita ma kasar Ruwanda tana sa ran karbar nata kason alluran daga kamfanin Pfizer karkashin shirin na COVAX.