1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal: Shekaru 60 da samun 'yanci

April 3, 2020

A wannan Asabar din hudu ga watan Afrilu, kasar Senegal da ke yankin yammacin Afirka ke bikin cikarta shekaru 60 da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na kasar Faransa.

Senegal Präsidentschaftswahlen | Macky Sall
Shugaba Macky Sall na senegalHoto: picture-alliance/Xinhua News Agency/D. Gueye

A wani jawabi da ya yi wa 'yan kasar ta Senegal a ranar 23 ga watan Maris din da ya gabata, shugaban kasa Macky Sall ya yi nuni da mawuyacin halin da ake ciki saboda cutar Coronavirus ko Covid-19, da ke ci gaba da yaduwa a duniya har ma da yammacin Afirka, yana mai cewa: "Ya ku al’umar kasata ina janyo hankulanku da cewa, ana cikin mawuyacin hali na rashin sanin tabbas. Cutar na yaduwa da sauri, abin da ya tilasta mana daukar matakai da suka dace, idan ba haka ba wani bala'i zai afka mana." 

Dage bikin samun 'yanci

Shugaban ya ayyana dokar ta-baci, sannan ya sanya dokar hana fita da daddare da ta fara aiki nan-take. Musulmi a kasar ba sa iya zuwa sallar Jumma'a, an kuma haramta taruwa a Majami'u kana an rufe makarantu da jami'o'i. Sannan an soke bikin cikar kasar shekaru 60 da samun 'yancin kai da ya kamata a yi a ranar hudu ga watan nan na Afrilu. Sojojin kasar ne kadai za su yi wani fareti. 

Alkaluman tsawon rai da mace-macen kananan yara a Senegal

Sai dai duk da haka kasar ta Senegal na da dalilai da dama na nuna farin ciki, inji Ute Gierczynski-Bocande mai kula da ayyukan gidauniyar Konrad-Adenauer ta Jamus a Senegal din, ta na mai cewa kasar ta samu gagarumin ci-gaba a fannin ilimi da fannin tattalin arziki. Ta kara da cewa koda yake bunkasar tattalin arzikin ta fi yin tasiri a Dakar babban birnin kasar, sai dai kuma gwamnati na yin wasu ayyuka domin rage tazarar ci-gaban tattalin arzikin tsakanin Dakar din da sauran yankunan kasar.

Tun kimanin shekaru 30 ke nan jami'ar ta gidauniyar Konrad-Adenauer ke zaune a Senegal, a cewar Ute Gierczynski-Bocande duk da ci-gaban har yanzu kasar na fama da talauci da rashin daidaito a cikinta, inda mizanin auna ci-gaban al'umma na Majalisar Dinkin Duniya ya saka kasar a matsayin ta 166 daga cikin kasashe 189.

Arzikin dan Ghana ya zarta na dan Senegal, kasar na samun ci-gaba

Shugaba Sall ya yi tazarce

A bara mafi rinjaye na al'ummar kasar sun sake zabar Shugaba Macky Sall a wa'adi na biyu. A dangane da sauyin mulki ta hanyar dimukuradiyya da tsarin ja'iyyu da yawa da kuma kwanciyar hankali da lumana musamman a siyasance, masana na masu cewa kasar ta Senegal ka iya zama abar koyi a yankin yammacin Afirka da ma wasu kasashen na nahiyar.