1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Senegal: 'Yan adawa sun yi zanga-zanga cikin lumana

February 17, 2024

Dubban 'yan adawa sun gudanar da zanga-zanga cikin lumana a birnin Dakar fadar gwamnatin Senegal domin nuna jin dadinsu a game da matakin kotun tsarin mulki na yin watsi da dage zaben shugaban kasar.

Senegal Protest in Dakar
Hoto: John Wessels/AFP

Masu zanga-zangar sanye da bakaken riguna sun yi ta daga alluna masu rubutun '' a mutumta jaddawalin zaben ranar 28 ga watan Fabarairu'', sai dai a wannan karo ba a samu arangama da jami'an tsaro ba sabanin boren da aka yi a kwanakin baya kan gage zaben.

Shugaba mai barin gado Macky Sall wanda wa'adin mulkinsa ke karewa a ranar biyu ga watan Aprilu mai zuwa ya ce ba tare da wata-wata ba zai aiwatar da umurnin da kotun tsarin mulki ta bayar na cewa a shirya zaben shugaban kasar cikin gajeren lokaci.

A karshen zanga-zangar 'yan adawan sun fidda sanarwa inda suka sha alwashin ci gaba da bijirewa duk wani yunkuri na yi wa kundin tsarin mulki kasar juyin mulki.