1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal za ta tusa ƙeyar tsohon shugaban ƙasar Cadi zuwa ƙasar sa

July 8, 2011

Hissène Habré tsohon shugaban ƙasar Cadi da ke yin gudun hijira a Senegal na shirin fuskantar tuhuma

Hissene Habre tsohon shugaban ƙasar CadiHoto: dpa

Shugaban ƙasar Senegal Abdulaye wade ya yanke shawarar tusa ƙeyar tsohon shugaban ƙasar Cadi Hissène Habré zuwa ƙasarsa ta asili.Sanarwar wacce gwamnatin ƙasar Cadi ta baiyana, ta ce za a turo tsohon shugaban ne a cikin wani tashin jirgin sama na musammun a ranar Litini mai zuwa idan allah ya kai mu.

Habre wanda ya jagoranci ƙasar Cadi daga shekara ta 1982 zuwa shekara ta 1990 wanda kuma ya ke zaman gudun hijira a Senegal tun daga wannan lokaci.Ana tuhumar sa da laifin keta hadin bil adama da kuma aikata gisan gila akan daruruwan jama'a

Mawallafi : Abdorahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu