Senegal: Zaben 'yan majalisun dokoki
July 28, 2017Zaben na zama wani muhimmin zakaran gwajin dafi na goyon baya ne gabanin zaben shugaban kasa da za'a yi a shekara ta 2019. A cewar fraiministan kasar Mohammed Boun Abdallah dai, yanzu an daina maganar zaben na ranar 30 ga watan Yuli, hankali ya karkata zuwa ga zaben shekara ta 2019.
Yakin neman zaben na wannan Lahadin ya yi zafi, ta yadda jami'an 'yan sanda suka rika zuba wa masu gangamin tayar da zaune tsaye hayaki mai sa hawaye. A yayin da ake tsare da mutane masu yawa, a wannan kasa da ke da tarihin demokaradiyyar zaman lafiya.
Shahararran mawakin nan na kasar ta Senegal Youssou Ndour, ya katse wani rangadi da yake a Turai domin dawo wa gida dan taimaka wa hadin gwiwar jam'iyyun da ke mulki a kasar. Sai dai a wata unguwa ta magoya bayan Khalifa Sall babban mai adawa da shugaban kasar Macky Sall, ayarin motocin Youssou Ndour ya sha ruwan duwatsu, inda aka samu mutane da dama da suka samu raunuka.