1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Senegal:Bassirou Diomaye zai karbi mulki daga hannun Sall

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 2, 2024

Mr Faye ya alkawarta yin iya kokarinsa wajen ganin an dawo da kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Nijar cikin ECOWAS, wadanda aka dakatar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasashen

Hoto: SEYLLOU/AFP

A Talatar nan za a rantsar da sabon shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye, wanda zai karbi mulki daga hannun shugaba mai barin gado Macky Sall, bayan samun nasarar lashe zaben da aka gudanar a kasar.

Karin bayani:Shugaban Faransa Emmanuel Macron na son kulla alaka da sabon shugaban Senegal

Daga cikin mahalarta taron bikin a birnin Dakar, akwai shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammcin Afirka ECOWAS, kuma shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da sauran shugabannin kasashen Afirka.

Karin bayani:Senegal: A hukumance an tabbatar da zababben shugaban kasa

Mr Faye ya alkawarta yin iya kokarinsa wajen ganin an dawo da kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Nijar cikin ECOWAS, wadanda aka dakatar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasashen.