1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLatin Amurka

Shakku kan sahihancin zaben Venezuela

Abdul-raheem Hassan SB
July 29, 2024

Yayin da kawayen Shugaba Maduro ke taya shi murnar cin zabe, kasashen duniya dama sun nuna shakku kan sahihancin zaben bayan sanar da Nicolas Maduro a matsayin wanda ya sake lashe zaben shugaban kasar kasar Venezuela.

Venezuela Caracas | Präsident Nicolas Maduro feiert Wahlergebnis
Hoto: Fernando Vergara/AP Photo/picture alliance

Shugaba Maduro ya sake lashe zaben shugaban kasar venezuela da kashi 51.2 cikin 100a cewar hukumar zaben kasar wacce yawanci ke biyyaya ga shugaban. Dan jam'iyyar adawa Edmundo Gonzalez Urrutia ya samu kashi 44.2 cikin 100, sai dai gammayyar jam'iyyun adawar sun ce yi ikirarin narasa da samun kashi 70 cikin 100 na kuri'u. Sai daiSakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya ce ko kusa sakamakon bai dace da zabin 'yan kasar Venezuela ba.

Karin Bayani: Venezuela: Shugaba Maduro ya lashe zabe karo uku

Jagoran 'yan adawa Edmundo Gonzalez da Maria Corina Machado bayan zaben VenezuelaHoto: Matias Delacroix/AP Photo/picture alliance

Sai dai Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya taya abokinsa Maduro murna, yana mai cewa dangantakar Kremlin da Venezuel na da tsarin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare. Dmitry Peskov shi ne kakakin fadar shugaban Rasha, wanda ya gaskata ingancin sakamakon zaben na Venezuela.

Venezuela na daya daga cikin kasashe uku da suka fito bayan rushewar Gran Colombia a shekarar 1830, tun daga wancan lokacin, an samu jajeyen wuyan sojoji da suka yi ta juya mulkin kasar har masana'antun man kasar suka habaka cikin sauri. Wannan ya sa dole a mutunta muradin al'ummar Venezuela da ke son kawo canji da kuri'u a cewar shugaban harkkokin waje na kungiyar Tarayyar Turai Joseph Borell. 

Gangamin zaben VenezuelaHoto: Matias Delacroix/AP Photo/picture alliance

A sanarwar da ta fitar, ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya, ta nuna damuwa ta rashin dai-dai da ake zargi a zaben tare da nuna bukatar adalci. Amma Beijin ta ce nasarar Maduro, dama ce ta sake karfafa hulda da Caracas don taimaka wa juna

Gwamnatin Peru ta kira jakadanta da ke Caras saboda zargin magudi a zaben, yayin da shugaban Costa Rika Rodrigo Chaves ya yi watsi da abinda ya kira aringizon kuri'u, Shugaban Chile Gabriel Boril ya yarda da nasarar Mudro abin mamaki ne. Luis Gilberto Murillo ya bukaci a sake tantance sakamakon, haka ita ma Argentina ta nuna wasan hannun riga da Maduro, amma 'yan gani kashenin shugaban na Latin Amirka kamar Cuba da Nicaragua da Bolivia da Hunduras ce cas ga masu adawa da nasarar Maduro karo na uku a matsayin shugaban kasar Venezuala da kasashen yamma ke wa kallon shugaban kama karya.