Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya sanar cewa za a kakaba wa Iran takunkumai mafi tsauri a tarihi. Sai dai take-taken gwamnatin Amirka karkashin jagorancin Donald Trump ba saboda tsaron Amirkar ba ne, buri shi ne a samu sauyin gwamnati a Iran, inji Matthias von Hein na tashar DW a cikin wannan sharhi.
Mike Pompeo ya zabi wuri mafi dacewa don yin jawabinsa na farko mafi girma kan manufofin ketare. A shekaru uku da suka wuce me sabon sakataren harkokin wajen na Amirka ya bayyana matsayinsa ka yarjejeniyar nukiliar Iran a gaban gidauniyar Heritage Foundation ta masu ra'ayin rikau.
A jawabinsa na ranar Litinin ma ya tabo batun amma a wannan karo bisa karfin ma'aikatarsa da goyon baya daga shugaban kasa. Dole ne a soki lamirin Iran dangane da abubuwan da take yi a yankin Gabas ta Tsakiya da ma yadda gwamnatin kasar ke gudana. Amma yin gaban kai da Pompeo ya yi a jawabin ya sanya shakku a ciki.
Gabatar da wasu batutuwa zababbu da yadda aka juya gaskiya ko ma watsi da ita ya sanya ayar tambaya ko za a samu wani ginshiki ba bai daya don tattaunawa tsakanin Turai da Amirka a kan batun na Iran.
Kalaman da ke fitowa daga Washington shi ne Amirka na son ta jagoranci wata tattaunawa, amma a gaskiya Pompeo da gwamnatin Trump ba su da alamar shiga wata tattaunawa, hasali ma matsin lamba suke na a yi aiki da ra'ayinsu ko an ki ko an so. Sharudda 12 da Pompeo ya gindaya wa gwamnatin Iran wani mataki ne na neman durkusar da tattalin arzikin kasar Iran din.