1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Fadi ba ta kare ba a Kamaru bayan Zabe

Mouhamadou Awal Balarabe GAT
February 11, 2020

A Kamaru, barazanar da 'yan aware suka yi ta far wa masu kada kuri'a da kuma kira na kaurace ma zabe da babbar jami'yyar adawa ta MRC ta yi, sun yi munmunan tasiri a tagwayen zabukan kananan hukumo da na 'yan majalisa,

Kamerun Präsidentschaftswahlen 2018
Hoto: Reuters/Z. Bensemra

A Kamaru, barazanar da 'yan aware suka yi ta far wa masu kada kuri'a da kuma kira na kaurace ma zabe da babbar jami'yyar adawa ta MRC ta yi, sun yi tasiri a tagwayen zabukan kananan hukumo da na 'yan majalisa, inda aka samu karancin masu kada kuri'a. Sai dai dimukuradiyya ba za ta kankama a Kamaru ba matikar ba a mangance matsalar sahihanci zabe da na barazanar tsaro da ke ci wa al'umma tuwo a kwarya ba, a cewar Mohd Awal Balarabe cikin sharhin da a rubuta mana.

Kwanaki uku bayan kada kuri'a ne ya kamata a samu cikakken sakamakon zaben kananan hukumomi a Kamaru, yayin da na 'yan majalisar dokoki kuma zai dauki kwanaki 20 kafin a bayyana wadanda suka yi nasara. Amma babu wani shakku cewar jam'iyyar RDPC ko CPDM ta Paul Biya ce za ta samu gagarumin rinjaye saboda akwai mazabu da dama da ita kadai ta tsayar da 'yan takara ba tare da hamayya ba. Wannan ya nuna cewar ta riga ta lashe kujeru 35 daga cikin 180 da majalisar dokokin Kamaru ta kunsa. 

Sai dai nasarar wannan tagwayen zabukan ta tattara ne kan adadin 'yan Kamaru da suka kada kuri’a daga cikin miliyan 6.800 da suka yi rejista. Dama babbar jam'iyyar adawa ta MRC ta bukaci magoya bayanta da su kaurace wa zaben, yayin da 'yan aware suka yi alkawarin sa kafar wando guda da duk wanda ya kuskura zuwa runfunan zabe a yankin Ingilishi, lamarin da ya kashe armashin zabukan tun ma kafin a gudanar da su.

Hoto: DW/M. Mefo


Amma ministan cikin gida Paul Atanga Nji ya bayyana cewar kirayen wadanda ya danganta da 'yan siyasa da ba sa kishin kasa da 'yan ta'adda na kaurace wa zabuka bai yi tasiri a zaben ba. Sai dai masu sa ido a zaben suka ce "ainihin wadanda suka kada kuri'a ba su fi kaso 25 cikin dari a sashe da ke magana da Faransanci ba, kuma yawan wadanda suka yi zabe bai kai haka ba a yankin Ingilishi.

Matakan tsaro da aka dauka a manyan birane na yankin Ingilishi kamar Buea da Bamenda da Limbe sun sa an samu damar kada kuri'a, sabanin kauyukan da masu zabe ba su fito ba sakamakon barazanar tsaro ta 'yan aware. Daidai da tsohon Firaministan kamaru Philemon Yang sai da ya yi amfani da helikofta da kuma rakiyar sojojin kundumbala na BIR a yankin Arewa maso Yamma kafin ya kada kuri'a.

Wannan zabe ya dada nunawa karara cewar har yanzu ba a dinke barakar da ke tsakanin 'yan aware da 'yan siyasa da masu mulki ba, duk da cewa an gudanar da tattaunawar kasa watanni ukun da suka gabata tare da sako 'yan siyasa da aka tsare. Daidai da dokar da ta bai wa yankunan Ingilishi matsayi na musamman da aka kafa bai sa an samu ci gaba mai ma'ana ba. Maimakon haka ma mutane na ci gaba da rasa rayukansu tare da kaurace wa matsugunansu sakamakon tabarbrewar harkokin tsaro, yayin da wasu 'yan adawa da ke da dimbim magoya baya ke yin buris da harkokin zabe, lamarin da ke dada durkusar da harkokin mulkin kasar tare da raba kawunan 'yan Kamaru. 

Kowanne daga cikin bangarori uku da ke da hannu a rikice-rikice a Kamaru ya samu biyan bukata, yayin da 'yan kasar da ita kanta ta samu koma baya. Gwamnati ta samu yawan 'yan majalisa da kananan hukumomi da zai sa ta ci gaba da cin karenta babu babbaka. Shi kuwa madugun 'yan adawa sun nuna cewar suna da karfin fada a ji da yawan masu na'am da gwagwarmayar da suka sa a gaba. Amma kuma tsayuwar gwamin jakin ya sa komai na tafiyar hawainiya, kuma 'yan kasa na dada kosawa da halayyar tsananin son kai da shugabanni ke nunawa.


Tabbas Kamaru na bukatar da zabe mai tsafta da zai sa a samu sauyin shugabanci bayan shekaru 38 na mulkin sai Mahdi ka ture da Paul Biya ke gudanarwa. Sai dai duk wani kwazo na neman inganta tsarin amfani da jam'iyyun barkatai zai tafi a uwa banza a Kamaru matikar dukkanin bangarorin da ke da hannu a rikicin ba su yi tattaunawar keke da keke tsakaninsu ba. Irin wannan zama ne zai sa a samar da tsarin zabe da zai magance matsalar aringizon kuri'i da ake zargin bangaren gwamnati da aikatawa, lamarin da kuma zai sa zabukan samun karbuwa ga kowa da kowa. A daya bangaren kuma, zaman sulhu da 'yan aware ne kawai zai samar da zaman lafiya da zai ba da damar shiryawa ba tare da kalubalen tsaro ba. Matikar wadannan ginshikai guda biyu na tsarin zabe da tsro ba su samu ba, Kamaru za ta ci gaba da zama 'yar baya ga dangi a fannin zabe da ci-gaban dimukuradiyya, lamarin da zai bai wa Paul Biya ci gaba da gudanar da salon mulkin sai Mahdi ka ture.